Arsenal ta fidda Liverpool daga FA

Arsenal FC Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal za ta karbi bakuncin Everton wasan daf dana kusa da karshe

Kungiyar Arsenal ta yi waje da Liverpool a kofin FA bayan data doke ta da ci 2-1 a wasannin zagaye na biyar.

Dan wasan Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain shi ne ya fara zura kwallo sannan ya haddasa kwallo ta biyu a wasan ramuwar gayya.

Liverpool ta doke Arsenal 5-1 a kofin Premier makon da ya gabata, amma wannan karon Oxlade-Chamberlain ne ya samu kwallo a minti na 16 ya kuma zura a ragar Liverpool.

Haka kuma shi ne ya haddasa kwallo ta biyu da Lucas Podoski ya zura a raga daga yadi na 15 bayan an dawo daga hutu.

Steven Gerrard ne ya zurawa Liverpool kwallonta a dukan daga kai sai mai tsaron raga.

Arsenal ta kai wasan daf dana kusa da karshe, za kuma ta karbi bakuncin Everton a watan Maris.