"Messi zai doke tarihin zura kwallo"

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya dawo ganiyarsa a fagen zura kwallaye

Kocin Barcelona Gerado Martino ya ce Lionel Messi zai doke duk wani tarihin zura kwallaye a raga, bayan da ya zama dan kwallo na uku a yawan zura kwallaye a tarihin gasar La Liga.

Messi mai shekaru 26 ya zura kwallaye biyu a karawar da suka doke Rayo Vallecano ranar Asabar, hakan yasa ya yi kankankan da tsohon dan wasan Real Madrid Raul Gonzalez da ya zura kwallaye 228 a La Liga.

Kwallaye 228 da Messi ya zura a raga a La Liga cikin wasannin 263, ya haura tsohon dan kwallon Real Madrid Alfredo De Stefano wanda ya zura kwallaye 227 a wasanni 359 da ya buga. Wadanda ke gaban Messi a yanzu sun hada da Telmo Zarra mai kwallaye 251da Hugo Sanchez mai kwallaye 234.

A duniya tuni ya kafa tarihin yawan zura kwallaye a kakar wasa guda, yawan zura kwallaye a duniya da kuma yawan zura kwallo a Shekara guda.

Saura kwallaye shida ya kama Raul, wanda ya zura kwallaye 71 a gasar kofin zakarun Turai.

Barcelona za ta kara da Manchester City a wasan 'yan kungiyoyi 16 da suka rage a kofin zakarun Turai, Martino na fatan Messi zai saka kaimi a wasan ganin dan kwallon ya zura kwallaye biyar a wasanni uku na bayan nan da ya buga.