Hamburg ta raba gari da Bert van Marwijk

Bert van Marwijk Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon kocin Holland da Hamburg ta sallama a bana

Hamburg ta sallami kocinta Bert van Marwijk, bayan da ya yi kwanaki 143 rike da ragamar kungiyar.

An sallami kocin tare da mataimakinsa Roel Coumans, bayan da Eintracht Braunsweig dake kasan tebur ta doke ta da ci 4-2 kuma rashin nasara ta bakwai da kungiyar ta yi.

Daraktan wasanni na kungiyar Oliver Kreuzer ya ce "Ya zama wajibi da muka dauki matakin, sai dai ba a son ran mu ba."

Hamburg ce kungiyar data buga kowacce kakar wasan Bundesliga tun lokacin da aka kirkiro gasar a shekarar 1963.

Sai dai a kakar bana itace kungiyar da akafi zurawa kwallaye a raga, domin an zura mata kwallaye 51 a wasanni 21, ranar Laraba ma sai da Bayern Munich ta zura mata kwallaye 5-0 a kofin Jamus.

Van Marwijk, tsohon kocin Holland, ya karbi ragamar horas wa a hannun Thorsten Fink ranar 24 ga watan Satumba.