Rooney na daf da tsawaita kwantiraginsa da United

Rooney Moyes Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zai ci gaba da wasa a United har zuwa shekarar 2019

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney na daf da tsawaita kwantiraginsa da kungiyar na tsawon shekaru biyar da rabi da kuma karin albashin £300,000 a kowanne mako.

Tuni United ta cimma yarje-jeniya da dan wasan mai shekaru 28 da zai ci gaba da buga mata kwallo a Old Trafford har zuwa Yulin 2019.

Rooney ya koma United ne dai daga Everton a Agustan 2004. Kwantaraginsa da United zata kare ne a karshen kakar wasan 2015 kuma yana daukar £250,000 a mako.

Sabunta kwantiragin Rooney a Old Traffofd zai kawo karshen rikita rikitar da dan wasan ya shiga tsakaninsa da tsohon koci Sir Alex Ferguson da yace dan wasan ya bukaci barin kungiyar a bara - zargin da dan wasan ya karyata.