Lacina na hangen lashe kofin FA a Everton

Lacina Traore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wasansa na farko ya zura kwallo da suka doke Swansea 3-1

Dan kwallon Ivory Coast Lacina Traore ya ce zai bada gudunmawarsa a Everton domin ta lashe kofin FA, bayan da ya zura kwallon a wasan farko da ya bugawa kungiyar a lokacin da suka doke Swansea.

Traore, wanda ya koma Toffees a matsayin aro daga Monaco a watan Janairu, ya zura kwallon farko da dunduniya a wasan da suka lashe da ci 3-1.

Dan wasan ya sanar ta yanar intanet din Everton yace "Abun murna ne ka fara wasan farko da zura kwallo, na yi farinciki."

Everton za ta ziyarci Arsenal a wasan daf dana kusa da karshe ranar takwas ga Maris, a lokacin Traore ya zai samu damar buga wasannin da zai murmure, ganin ya koma Goodison Park ne dai yana jinya.