Fernandinho na daf da komawa wasa

Fernandinho
Image caption Bayan jinyar da dan wasan ya yi zai dawo karawa da Barcelona

Dan kwallon Manchester City Fernandinho na daf da dawo wa wasa a gasar kofin zakarun Turai da kungiyar za ta karbi bakuncin Barcelona ranar Talata na zagaye na biyu.

Dan wasan mai buga tsakiya bai samu bugawa City wasanni uku baya ba, sakamakon jinya da ya yi amma ya soma atisaye da kungiyar ranar Ltinin.

Sai dai Sergio Aguero bai yi atisaye da sanyin safiyar Litinin ba, saboda haka ba zai buga karawar ba.

Dan wasan Argentinan rabonsa da bugawa City kwallo tun a ranar 29 ga Janairu bayan da ya ji rauni a karawar da suka doke Tottenham da ci 5-1.

Aguero, ya zura kwallaye 26 a wasanni 25 da ya buga a bana, sai sauya shi a kayi a wasan Spurs da ake hangen zai yi jinyar wata guda.

Dan wasan mai shekaru 25 ya koma wasa bayan da bai samu buga wasanni takwas a raunin da ya ji a gwiwa kafin kuma ya sake jin wani raunin kwanan na.