Rooney zai zauna a Man U har 2019

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rooney zai rika samun £300,000 a mako.

Ana tsammanin Wayne Rooney zai sanya hannun wani sabon kwanturagi na shekaru biyar da rabi tare da Manchester United a wannan makon.

Hakan kuma zai sa albashin sa ya karu zuwa kusan £300,000 a mako.

Dan wasan Ingilan mai shekaru 28 a duniya yana daf da kulla wannan kwanturagi tare da Kulab din har zuwa shekara ta 2019.

Rooney dai ya hade da United ne daga kulab din Everton a watan Agustar shekara ta 2004.

Kuma yanzu haka yarjejeniyar sa da kulab din zata kare ne a lokacin bazarar shekarar 2015.

Yana kuma karbar £250,000 a mako guda a yanzu.