'Babu tabbas kan Cole a Chelsea'

Ashley Cole Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan na fama da kalu bale a Chelsea da Ingila

Jose Mourinho ya bayyana kila-wa-kala game da makomar dan wasan Ingila mai tsaron baya Ashley Cole a Chelsea bayan da yaki fayyace ko zai dinda sa dan kwallon a wasa.

Kwantaragin Cole za ta kare da Chelsea a karshen kakar bana, kuma Cesar Azpilicueta ne ke buga gurbinsa a Chelsea.

Dan wasan mai shekaru 33 yana fama da kalubalen samun gurbin bugawa tawagar Ingila wasa a kofin duniya.

Da aka tambayi Mourinho ko zai dinda sa Cole a wasanni, sai ya ce " Ban sani ba. Amma ina farinciki da yadda Azpilicueta yake kwazo a wasannin mu.

Rabon Cole ya buga Premier tun 11 ga Janairu da Chelsea ta kara da Hull, kuma bai buga kofin FA da Manchester City ta lashe wasan ranar Asabar, tuni ake rade-radin dan wasan zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

Cole ya bugawa Ingila wasanni 106, sai dai yana samun kalubale a wajen dan wasan Everton Leighton Baines.

Kocin Ingila Roy Hodson kila ya yi amfani da Luke Shaw dan wasan Southampton da dan kwallon Arsenal Kieran Gibbs a wasan sada zumunci da za su kara da Denmark ranar 5 ga Maris.