CSKA za ta buga wasa ba 'yan kallo

CSKA Moscow Hakkin mallakar hoto AP
Image caption CSKA ta yi kaurin suna wajen kalamun batanci da wariya

Kungiyar CSKA Moscow dake Rasha za ta buga wasanta na gaba na kofin zakarun Turai babu 'yan kallo, bayan da magoya bayanta suka ci gaba da halayyar batanci ga 'yan wasa.

A Nuwamba sai da aka umarci kulob din ya rufe wani sashi na 'yan kallo, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi wa Yaya Toure dan kwallon Manchester City kalamun wariya a karawar da suka yi a Oktoba.

Magoya bayan kungiyar sun ci gaba da halayyar kalamun wariya da cin mutuncin 'yan wasa ta nuni da yatsa a Disamba lokacin da suka kara a kofin zakarun Turai a Viktoria Plzen.

Haka kuma an ci tarar CSKA kudi £41,200.