Kosovo ta gayyaci Januzaj wasa

Adnan Januzaj Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan wasan yana da damar zabar kasar da zai bugawa wasa

Kosovo ta gayyaci dan kwallon Manchester United Adnan Januzaj ya buga mata wasa a karon farko, a wasan sada zumunci da za ta kara da Haiti ranar 5 ga Maris.

Januzaj, mai shekaru 18 zai iya bugawa kasashen Albania ko Belgium ko Turkiya ko Serbia da kuma Ingila idan sun gayyace shi.

Idan Januzaj ya bugawa Kosovo wasa ba zai raunata bugawa kasar da zai zaba ba, saboda sai babban wasa ne yake hana dan wasa bugawa wata kasa.

Fifa ta yanke hukunci a watan jiya cewa Kosovo wacce ba mamba bace a majalissar dinkin duniya za ta iya buga wasan sada zumunci amma banda kasar da ta fito daga tsohuwar Yugoslavia.

Sai dai baza su bayyana alamar kasar suba, sannan ba za a kada taken kasarba kuma wasan Fifa ba zata kirga shi ba a fitatcen wasa.