Fifa ta ci tarar Zambia kan karya ka'ida

Fifa Logo
Image caption Kungiyoyin kwallon Zambia ne suka yi musaya 'yan kwallo ba bisa ka'ida ba

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ci tarar Zambiya kan karya ka'idar musayar 'yan kwallo.

Fifa ta sanar ranar Laraba cewa ta ci tarar hukumar kwallon kafa ta Zambia $56,000 sakamakon cinikin kwararrun 'yan wasa uku da 'yan wasa masu tasowa biyar ba tare da cikakkun takardu ba kuma bayan an rufe kasuwar musayar 'yan kwallo.

Haka kuma an hukunta kungiyoyin kasar su uku bisa cinikin 'yan wasan ba bisa ka'ida ba.

An ci tarar Zanaco $22,500 yayin da Power Dynamos da National Assembly kuma aka ci su tarar $25,000.

A Oktoban 2010 ne Fifa ta kara tsaurara ka'idojin musayar 'yan kwallo.