“ Erickson ya goyi bayan Barcelona”

Manuel Pellegrini

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Barcelona ta lallasa Manchester City da ci 2-0 a Etihad.

Mai horar da 'yan wasan Manchester City Manuel Pellegrini ya ce Alkalin wasa Jonas Erikson ya goyi bayan Barcelona a wasan da suka samu nasara akan Manchester City da ci 2-0 a filin wasa na Etihad.

Alkalin wasa Erikson dai ya baiwa Barcelona bugun ‘daga kai sai mai tsaron gida’ sannan ya kori mai tsaron bayan City Martin Demichelis.

Don haka ne ma Pellegrini ya yi ikirarin cewa Erikson ya nuna son kai.

Yace ‘yana bayan Barcelona daga farkon wasan har karshe’