An sallami Laudrup ne ta sakon E-Mail

Micheal Laudrup Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Laudrup yana mamakin yadda suka raba gari da Swansea

Tsohon kocin Swansea City, Michael Laudrup, ya ce an sallame shi daga aiki ne ta hanyar wasikar da aka aike masa ta Intanet.

Hakan ya faru ne awanni kadan bayan taron ya yi da shugaban kungiyar Huw Jenkins, wanda ya tabbatar masa da aikinsa sannan suka sha hannu.

Laudrup, mai shekaru 49, ya jagoranci kungiyar da ta lashe League Cup a bara, kofinta na farko a shekaru 102 da kafa kungiyar.

Swansea ta raba gari ne da kocin bayan da kungiyar ta kasa taka rawar gani a kakar bana da cece kuce a kan mataimakansa a lokacin.

Laudrup ya kara da cewa, "Lamarin ya faru ne bayan awanni da muka yi hannu da shugaban kungiyar; ina cike da mamakin faruwar hakan."