Uefa na binciken Pellegrini

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Uefa na bincikie idan ya dace a ladabtar da kocin

Hukumar kwallon Turai Uefa na binciken kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, bisa kalaman da ya yi cewa alkalin wasa ya nuna son kai a wasan da Barcelona ta doke su da ci 2-0.

Alkalin wasa Jonas Erikson dan Sweden ya bada jan kati ga dan wasan City Domichiles da Penarity a gasar kofin zakarun Turai da suka kara ranar Talata.

Uefa ta ce ta nada jami'in da zai binciki kalaman kocin idan za a iya daukar matakin ladabtarwa akansa.

Hukumar ta ce, sai bayan an kammala bincike ne za ta bude zama don ta dauki matakin ladabtarwa.