Romeu ya zama kocin Angola

Image caption 'Yan kwallon Angola

Angola ta nada Romeu Filemon a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallonta.

Dan shekaru 49, ya maye gurbin dan kasar Uruguay Gustavo Ferrin wanda aka kora bayan ya kasa tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Brazil da za a buga a bana.

Romeu wanda ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu, zai maida hankali wajen tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za a buga Morrocco.

A baya, Romeu ya taba aiki tare da kungiyoyi daban-daban a kasar ta Angola.

Wasansa na farko a matsayinsa na koci zai kasance na sada zumunci tsakaninsu da Mozamboque a Maputa a ranar 5 ga watan Maris.

Karin bayani