UEFA: Pellegrini ya nemi afuwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin City, Manuel Pellegrini

Manuel Pellegrini ya nemi afuwa saboda sukar alkalin wasa, bayan da Manchester City ta sha kashi a wajen Barcelona a gasar zakarun Turai.

Kocin kasar Chile din ya caccaki alkalin wasa dan kasar Sweden Jonas Eriksson a kan cewar ya goyi bayan Barca a wasan da aka buga a filin Etihad.

Tuni dai hukumar kwallon Turai Uefa ta soma binciken kalamansa.

Pellegrini yace "Muna yi rashin nasara a wasan, shi yasa na yi fushi".

An kori Martin Demichelis a wasan bayan ya kayar da Lionel Messi abinda ya sa aka baiwa dan Argentina din bugun fenariti.

Karin bayani