Ozil na cikin bacin rai - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mesut Ozil ya yi takaicin barar da kwallo

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce har yanzu dan kwallonsa Mesut Ozil yana cikin damuwa bayan da ya kasa cin bugun fenariti a wasansu da Bayern Munich.

Ozil mai shekaru 25, wanda ya fi kowa tsada a tarihin kungiyar, ya nemi afuwa a shafinsa na Facebook bayan ya barar da bugun fenariti.

Wenger ya ce har yanzu Ozil bai gama murmurewa ba daga tunanin rashin nasarar.

Ozil ya koma Arsenal daga Real Madrid a kan fan miliyan 42.5 a watan Satumbar 2013, amma a 'yan watannin nan yana shan suka game da salon taka ledar sa.

Karin bayani