Mamelodi Sundowns ta dauki Uzoenyi

Ejike Uzoenyi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai a watan Yuni ne dan wasan zai koma Mamelodi Sundowns

Kungiyar Mamelodi Sundowns ta Afirka ta kudu ta bada tabbacin daukar dan kwallon Najeriya Ejike Uzoenyi.

Dan wasan mai shekaru 24, shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da yafi fice a gasar kofin Afirka ta 'yan wasa dake taka leda a Afirka wato Chan 2014 da Afirka ta kudu ta karbi bakunci.

Dan kwallon Enugu Rangers ta Najeriya ya rattaba kwantiragin shekaru hudu da kungiyar.

Nan take an bada Uzoenyi aro ga Enugu Rangers, kafin watan Yuni da zai koma Tshwane dungurungum.