'Rooney bai damu da kuwar Palace ba'

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Magoya bayan Palace sune kuma za suyi masa sowa a kofin duniya

Kocin Manchester United David Moyes ya ce Wayne Roony bai damu da kuwwar da magoya bayan Crystal Palace suka yiwa dan wasan ba domin sune za suyi masa sowa a kofin duniya.

Dan kwallon Ingila wanda ya tsawaita kwantiraginsa da United tsawon shekaru biyar da rabi, wasu magoya bayan Palace sun jefe shi da kwandaloli kafin aje hutu lokacin United ta zura kwallaye 2-0.

Moyes ya ce "Nan da watanni uku masu zuwa wadannan 'yan kallon za suyi masa sowa da tafi, yakan faru a kowanne lokaci kuma kwararren dan wasa ne, nasan bai damu ba ko kadan."

Game da tsawaita kwangilar Rooney da United Moyes ya kara da cewa "Mun yi murna matuka, ace sayo Rooney za muyi daga waje zai yi tsada balle idan baka da kudi a kasa."