'Rosicky zai ci gaba da wasa a Arsenal'

Tomas Rosicky Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan ya sha fama da jinyar rauni a Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya hakikance cewa mai wasan tsakiya Tomas Rosicky zai tsawaita kwantiraginsa da kungiyar idan yarjejeniyar da suka kulla ta cika.

Dan kwallon mai buga tsakiya mai shekaru 33, ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a shekarar 2006, kuma kwantaraginsa za ta kare da Arsenal a karshen kakar wasan bana.

Dan wasan Czech ya yi bajinta a gurbin da ya maye Mesut Ozil wanda yake jinya a karawar da suka doke Sunderland da ci 4-1 ranar Asabar.

Wenger ya ce "Tomas Rosicky zai ci gaba da wasansa a Arsenal, mun cimma yarjejeniya da zai tsawaita kwantiragi da mu kwanan nan."

Rosicky, wanda ya sha fama da jinya a kungiyar dake Arewacin Landan, ya samu yabo daga Wenger a yadda ya saka hazaka a wasan da suka doke Sunderland, har ma ya zura kwallo ta uku a raga.