Barca ta biya harajin £11.2m kan Neymar

Neymar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan kwallon ya kagu a kammala rikita-rikitar dake tsakanin cinikinsa

Barcelona ta biya Spain harajin £11.2 miliyan, bayan da aka zargeta da kaura cewa biyan haraji a cinikin Neymar

Koda yake Barca ta nace akan cewa bata karya wata ka'ida ba.

Kungiyar ta biya Santos £48.6 miliyan kan daukar dan wasan mai shekaru 22, a bara da kuma baiwa iyayensa £34 miliyan

A tsakanin kudin hakikar daukar dan kwallon dana rattaba kwantaragi da albashinsa da aka kulla kan shekaru biyar da kudin eja, kudin haraji da Barcelona ya kamata ta biya zai kai £106.8m

A watan jiya ne dai shugaban kungiyar Sandro Rosell ya yi murabus bisa zargin da ake masa kan almubazzaranci da kudi.