Pique zai buga karawa da Man City

Gerard Pique Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan na fatan Barcelona za ta lashe City a karawa ta biyu

Ana sa ran mai tsaron bayan Barcelona Gerard Pique zai dawo daga jinyar da ya ke yi domin fuskantar Manchester City a karawa ta biyu a wasan zagaye na biyu na kofin zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 27 ya ji rauni ne dai a chinyarsa da ya tafi jinyar mako biyu a karawar da Real Sociedad ta doke su da ci 3-1 ranar Asabar.

Barca za ta karbi bakuncin City ranar Laraba 12 ga Maris, Barcelona ce ta doke City a Ettihad da ci 2-0 a karawar farko.

Pigue, ya bugawa Barcelona wasanni 33 a kakar bana, kungiyar dake matsayi na biyu a teburi La liga bayan da Real Madrid ke samanta da tazarar maki uku.