Kenya za ta karbi bakuncin CHAN 2018

Chan Kenya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Gasar Chan na samun karbuwa daga kasashen Afirka

An zabi Kenya ta karbi bakuncin kofin Afirka ta 'yan kwallon dake taka leda a Afirka Chan 2018,

Kasar za ta zamo ta biyu daga shiyyar gabashi da tsakiyar Afirka da zata karbi bakuncin gasar da ake fafatawa tsawon mako uku, Rwanda ce za ta karbi bakuncin gasar 2016.

Libya ce ta lashe karo na uku da aka gudanar a Afirka ta kudu a Fabrairu, bayan da ta doke Ghana a bugun Fenarity a wasan karshe.

Dr Congo ce ta lashe karon farko a shekarar 2009, Tunisia ta zama zakara a shekarar 2013.