Nasri na tsoron rasa kofin Capital One

Samir Nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun a farko Pellegrini ya ce kungiyar na harin lashe kofuna hudu

Samir Nasri na fatan shirin da Manchester City take na lashe kofuna hudu, kada su bi ruwa kamar na Arsenal lokacin da ta hari daukar kofuna hudu a shekarar 2011.

Nasri, wanda kungiyarsa City za ta kara da Sunderland a wasan karshe a Capital One Cup, yana cikin 'yan wasan Arsenal da Birmingham ta doke a wasan karshe a shekarar 2011 kafin su gaza daukar kofi a shekarar.

Nasri ya kara da ce wa "Na san radadin da naji da aka doke mu a wasan karshe a Carling Cup lokacin ina Arsenal.

"Bayan wasan ne muka lashe wasanni biyu a Premier, saboda haka lashe kofin shi ne mafi alfanu"

Arsenal tayi rashin nasara a hannun Barcelona a kofin zakarun Turai wasan zagaye na biyu, sannan Manchester United ta doke ta a kofin FA wasan zagaye na shida.

Chelsea mai matsayi na daya a teburi ta bawa City tazarar maki uku, sai dai tana da kwantan wasa da Sunderland, sannan tana cikin kofin FA wasan daf dana kusa da karshe.