Nigeria: An nada Manu Garba kochi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar kwallon kafar Nigeria ta yi nade-nade

An bayyana sunan Manu Garba wanda ya jagoranci ‘yan wasan Nigeria zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 17 a UAE a bara a matsayin sabon kochin ‘yan kasa da shekaru 20.

Magoya bayan ‘yan wasan Nigeria dai na cikin gida na matukar girmama Garba bayan da ‘yan wasan Kasar ‘yan kasa da shekaru 17 suka zo na hudu bayan nasarorin da suka samu a China a 1985 da Japan a 1993 da kuma Korea ta Kudu a 2007.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta kuma amince da nada tsohon dan wasan duniyar nan Emmanuel Amuneke a matsayin sabon kochin ‘yan kasa da shekaru 17.

Tsohon dan wasan duniyar nan Nduka Ugbade ne zai taimakawa Manu Garba a sabon mukamin nasa.