Mourinho ya soki nadar murya a boye

Jose Mourinho
Image caption Kocin ya ce 'yan jarida sun yi abin kunya da suka nadi jawabinsa ga 'yan wasa cikin sirri

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce abin takaici ne da aka nadi muryarsa a boye aka watsa a talabishin Faransa lokacin da yake kalubalantar 'yan wasansa masu zura kwallo a raga.

Kocin ya kara da ce wa yana raha ne lokacin da yake korafin rashin zura kwallo a raga da masu zura masa ba sa yi, har ma ya yi barkwanci a kan shekarun Samuel Eto.

Mourinho ya ce "Abin dariya ne ka tattauna da wanda ba ya cikin duniyar kwallon kafa -- kuma cin mutunci ne wani ya nadi murya hirar wasu a cikin sirri."

Da ake tattaunawa da shi a kan karawar da za su yi da Galatasaray a kofin zakaru, Mourinho ya shaida wa 'yan jarida cewa sun ji kunya ta yadda kafar mujallar Canal Plus ta ruwaito jawabin da ya yi a kan 'yan wasansa cikin sirri kwanaki takwas da suka wuce a Switzerland.

An ruwaito Mourinho yana cewa "Matsalar Chelsea bai wuce kasa zura kwallo a raga ba. Ina da Eto'o mai shekaru 32, kila ma shekarunsa 35, wa ya sani?