United na cikin matsi - kocin Olympiakos

Moses Olympiokos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin ya ce a shirye suke na ganin sun lashe United

Kocin Olympiakos Michel ya ce abokiyar karawarsu Manchester United a kofin zakarun Turai wasan zagaye na biyu, tana cikin matsi bisa rashin kokarin da take a kofin Premier.

An ba wa United tazarar maki 11 tsakaninta da masu neman gurbin shiga kofin zakarun Turai a Premier, kocin dan Spain ya kara da cewa kungiyar za ta fuskanci kalubale a filin Karaiskakis.

Micheal, mai shekaru 50, ya ce "Irin wannan yanayin da suke ciki zai sa 'yan wasa su dauki nauyin lashe karawar a kansu."

Golan Olympiakos Roy Carroll tsohon dan kwallon United da ya taka mata leda daga 2001 zuwa 2005 ya ce "United a tsorace take da karawa da za mu yi."

Michel ya kara da cewa za su baiwa United mamaki, tunda har suka samu fitowa zagaye na biyu daga rukunin da ya kunshi Paris St-Germain da Benfica da Anderlecht.

Za su kara a wasa na biyu a filin Old Trafford ranar 19 ga Maris.