Aguero ya dawo Atisaye bayan jinya

Dan wasan Manchester City Sergio Aguero, kila ya buga wasan karshe a kofin Capital One ranar Lahadi, bayan da ya dawo atisaye ranar Talata daga jinya.

Dan kwallon Argentina rabonsa da buga wasanni tun tsawon makwanni da suka wuce, bayan da ya ji rauni a karawar da suka doke Tottenham da ci 5-1.

Tsawon jinyar da dan wasan ya yi, City ta zura kwallaye a wasanni uku daga cikin wasanni biyar data buga.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya sha jinyar sama da mako guda

Aguero, mai shekaru 25, ya buga atisaye cikin koshin lafiya, kila ya buga wasan karshe a Capital One da Sunderland a Wembley ranar Lahadi.