Murray ya doke Andujar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Murray zai fuskanci Joao Sousa

Dan Burtaniyan nan mai buuga wasan Tennis Andy Murray ya doke dan wasan Kasar Spain Pablo Andujar 3-6 6-1 6-2 a zagayen farko na gasar Mexican Open.

Ana gudanar da wannan gasa ne a Acapulco.

A yanzu dai zai fuskanci dan wasan Portugal Joao Sousa.

A waje daya kuma a Dubai, James Ward ya doke dan kasar Russia Teymuraz Gabashvili da 2-6 6-4 7-6 (8-6)