Adidas ya janye rigunan batsa na Brazil

Adidas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumomin Brazil sun ce rigunan da kamfanin Adisad ya yi za su janyowa kasar bacin suna.

Kamfanin da ke samar da rigunan 'yan wasan kwallon kafa mai suna Adidas ya ce zai daina sai da rigunan gasar cin kofin duniya na batsa, bayan da hukumomin kasar Brazil suka ce ya na tallata ayyukan fasadi a kasar.

An rubuta '' kana bukatar cin kwallo'' a gaban wata riga, a gefenta kuma wata mace ce da ta bayyana tsiraicinta.

Wata rigar kuma an yi zanen hoton zuciya da ya yi kama da mazaunan mace an kuma rubuta "Ina son Brazil" a cikin zanen.

Hukumomin yawon bude idanun Brazil sun ce hakan zai iya batawa kasar suna.

Karin bayani