Defoe zai yi ban kwana da Tottenham

Jermain Defoe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Defoe zai koma Amurka da buga kwallo

Jermain Defoe ba zai buga wasansa na karshe da Tottenham ba a kofin zakarun Turai wato Europa League wasan zagaye na biyu da za su kara da Dnipro, sakamakon raunin da ya yi.

Dan kwallon Ingila mai shekaru 31, zai koma kungiyar Toronto dake Amurka ranar Juma'a, bayan da Spurs ta sayar da shi kan £6 miliyan a watan jiya.

Sandro mai wasan tsakiya da Kyle Walker 'yan wasan Tottenham sun gama jinya za su buga karawa da Dnipro wacce ta lashe wasan farko da ci daya mai ban haushi.

Sai dai kuma Danny Rose da Etienne Capoue suma na Spurs ba za su buga karawar ba, sakamakon raunin da suka ji a wasan da Norwich ta doke su da ci daya mai ban haushi ranar Lahadi.

Defoe zai yi ban kwana da magoya bayan kungiyar ne, bayan da aka shirya cewa zai fito tsakiyar filin wasan White Hart Lane bayan an tafi hutun wasa a karawar ranar Alhamis.

Dan wasan shi ne na biyar a yawan zura kwallaye a gasar Premier, bayan da ya zura kwallaye 143 daga cikin wasanni 363.