Kocin West Brom Mel na cikin matsi

Pepe Mel
Image caption Wasanni shida ya kara da har yanzu bai lashe wasa ba

Kocin kungiyar West Brom Pepe Mel na cikin tsaka-mai-wuya na ganin ya tsawaita aikinsa a kungiyar, bayan da ya jagoranci wasanni shida a gasar Premier.

Dan kasar Spain ya karbi ragamar kocin kungiyar ranar 9 ga Janairu, har yanzu bai lashe wasa ba, bayan buga wasanni shida a karkashinsa, kuma saura maki daya ya fado sahun kungiyoyin da za su iya barin gasar Premier a bana.

Manyan 'yan kwallon kungiyar sun bayyana damuwarsu kan Mel mai shekaru 50, da salon yadda yake horar da 'yan wasa.

Shugaban kungiyar Jeremy Peace ya ce a shirye yake ya dauki duk wani mataki da zai fitar da kungiyar daga halin data tsinci kanta.

Kungiyar za ta karbi bakuncin Manchester United a filinta na The Hawthorns, ranar Asabar.