"Muna girbar rashin zura kwallaye"

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan gaba na kungiyar suna karancin zura kwallaye a raga

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce kungiyarsa na girbar rashin zura kwallo a raga, bayan da suka tashi wasa 1-1, a karawar da suka yi da Galatasaray a kofin zakarun Turai.

Chelsea wacce take matsayi na daya a teburin Premier, ita ce ta fara zura kwallo ta hannun Fernando Torres a Istanbul.

Bayan an dawo daga hutu Galatasaray ta farke kwallonta, hakan na nufin karawa ta biyu da za su buga ranar 18 ga Maris ta zama ta mai rabon kaiwa wasan daf dana kusa da karshe.

Mourinho ya ce "Wasu kungiyoyin suna samun damarmaki karo uku, su zura kwallaye ukun a raga, mun samu damarmaki karo biyar mun zura kwallo daya kacal a raga.