Ingila ta gayyaci Shaw cikin tawagarta

Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan na fatan taka rawa a wasan sada zumuncin

Ingila ta gayyaci dan wasan Southampton Luke Shaw, cikin tawagar 'yan kwallonta 30 da za su kara da Denmark a wasan sada zumunci ranar Laraba a Wembley.

Dan wasan mai shekaru 18, ya samu goron gayyata ne tare da dan kwallon Liverpool Raheem Sterling mai shekaru 19, da Ross Barkley mai shekaru 20, dan kwallon Everton mai wasan tsakiya.

Kocin Ingila Roy Hodson, ya kuma kara gayyato dan wasan Cardiff City mai tsaron baya Steven Caulker, mai shekaru 22, rabonsa da bugawa Ingila wasa tun karawar da suka sha kashi a hannun Sweden da ci 4-2 a wasan sada zumunci a Nuwambar 2012.

Sai dai kocin bai gayyaci dan wasan Sunderland Adam Johnson da Gareth Barry dan kwallon Everton ba.

Ga 'yan wasan da Ingila ta gayyata buga wasan sada zumunci

Masu tsaron raga: Fraser Forster (Celtic), Ben Foster (West Bromwich Albion), Joe Hart (Manchester City), John Ruddy (Norwich City).

Masu tsaron baya: Leighton Baines (Everton), Gary Cahill (Chelsea), Steven Caulker (Cardiff City), Ashley Cole (Chelsea), Glen Johnson (Liverpool), Luke Shaw (Southampton), Chris Smalling (Manchester United), Kyle Walker (Tottenham Hotspur).

Masu wasan tsakiya: Ross Barkley (Everton), Michael Carrick (Manchester United), Tom Cleverley (Manchester United), Steven Gerrard (Liverpool), Jordan Henderson (Liverpool), Adam Lallana (Southampton), Frank Lampard (Chelsea), James Milner (Manchester City), Alex Oxlade-Chamberlain (Arsenal), Raheem Sterling (Liverpool), Andros Townsend (Tottenham Hotspur), Jack Wilshere (Arsenal).

Masu zura kwallo: Jermain Defoe (Toronto FC), Rickie Lambert (Southampton), Jay Rodriguez (Southampton), Wayne Rooney (Manchester United), Daniel Sturridge (Liverpool), Daniel Welbeck (Manchester United)