Matuidi ya tsawaita kwantaraginsa da PSG

Blaise Matuidi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce PSG za tayi fice da kuma lashe kofuna a bana

Dan kwallon PSG mai wasan tsakiya Blaise Matuidi, ya tsawaita kwantiraginsa da PSG, da zai ci gaba da wasa a kungiyar zuwa shekarar 2018.

Dan wasan mai shekaru 26, kwantaraginsa zai kare da kungiyar ne a kakar wasan bana, an yi rade -radin Manchester City ta so ta dauki dan kwallon a bana.

Ya amince da tsawaita kwantiraginsa da PSG ne, sati guda da Thiago Motta shi ma ya cimma yarjejeniyar ci gaba da bugawa kungiyar wasanni.

Matuidi ya buga wasanni 124 ya zura kwallaye 13, tun lokacin da ya koma kungiyar daga Saint-Etienne a shekarar 2011.

PSG, tana matsayi na daya a teburin gasar Faransa, ta bada tazarar maki biyar, kuma tana harin kaiwa wasan daf dana kusa da karshe a kofin zakarun Turai bayan data doke Leverkusen da ci 4-0 har gida.