"Matsayinmu na rikon kwarya ne"

Jose Mourinho
Image caption Mourinho kamar yadda ya saba ya ce dakwan teburi su keyi

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce matsayin da kungiyarsa ke kai, na daya a teburin Premier, na rikon kwarya ne.

Chelsea ta doke Fulham da ci 3-1 ranar Asabar, lokacin da Arsenal ta yi rashin nasara a filin Britania inda aka doke ta da ci daya mai ban haushi.

Hakan na nufin Chelsea tana matsayi na daya a teburi bayan da ta bai wa Liverpool da Arsenal wadanda su ke matsayi na biyu da na uku tazarar maki hudu da tazarar maki shida tsakaninta da Manchester City.

Mourinho ya ce "Tazarar makin da muka bayar a Premier ga City ba komai ba ne, da zarar sun lashe kwantan wasanninsu biyu da ba su buga ba, domin sun fi mu yawan zura kwallaye a raga.

Manchester City tana da maki 57 daga cikin wasanni 26 da ta buga, Chelsea kuwa tana da maki 63 daga wasanni 28.