"Da ni fari ne da Ingila ta ban Kyaftin"

Sol Campbell
Image caption Hukumar kwallon Ingila ta san da korafin amma ba ta ce komai ba

Tsohon dan wasan Ingila Sol Campbell ya ce da shi farar fata ne, da Ingila ta ba shi kyaftin din tawagar kasar shekaru goma baya.

Cambell ya yi wannan korafin ne a labaran rayuwarsa wanda ba a ba da izini ba, da mujallar Sunday Times take wallafawa jifa - jifa.

Mai shekaru 39, wanda ya buga mata kwallaye karo 72 da wasanni uku a matsayin kyaftin ya ce "Na tabbata da ni farar fata ne da na zama kyaftin din tawagar 'yan wasan Ingila shekaru goma baya -- gaskiyar lamari ke nan."

Hukumar kwallon kafar Ingila FA, tana sane da zargin, amma ba ta ce komai ba.