Madrid da Atletico sun tahi wasa 2-2

Madrid Atletico Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasan hamayya sun tashi kowa nada maki a tsakaninsu

Real Madrid ta raba maki da Atletico Madrid a wasan hamayya da suka kara ranar Lahadi, sun tashi wasa 2-2 a karawar da su kayi a filin wasa na Vicente Calderon Stadium.

Karim Benzema, ne na Madrid ya fara zura kwallo a ragar Atletico, amma Koke ya farke kwallo.

Kyaftin din Atletico Gabi ya kara kwallo ta biyu kafin a tafi hutu a bugun dake da tazara kuma kwallo ta fada raga.

Sai dai Ronaldo, ya farke wa Madrid kwallo da hakan ke nuna cewa sun raba maki a tsakaninsu.

Real Madrid tana da maki 64 bayan wasanni 26, ita kuwa Atletico Madrid tana da maki 61 bayan wasanni 26 data buga.