Taylor bai amince da zargin Campbell ba

sol Campbell
Image caption Tsohon dan kwallon ya zargi an hana shi kyaftin saboda launin fata

Tsohon kocin Ingila Graham Taylor ya karyata zargin da Sol Campbell, ya yi na cewar ba a zabe shi a kyaftin din tawagar 'yan wasan kasar ba, bisa dalilin bambancin launin fata.

Cambell, mai shekaru 39, ya hakikance da ce wa da shi farar fata ne da tuni an bashi kyaftin din tawagar kasar shekaru 10 baya da suka wuce.

Sai dai Taylor, wanda ya horas da Ingila daga shekarun 1990 zuwa 1993 bai amince da zargin ba.

Ya shaidawa BBC ce wa "Ban taba zabar kyaftin ba bisa fifiko kan banbancin launin fata ba".

Taylor shi ne ya fara zabar mai wasan tsakiya Paul Ince, bakar fata na farko da ya zama Kyaftin din tawagar kasar a zamaninsa.