Gasar cin Kofin duniya saura kwana 100

Daya daga cikin filayen wasan da za a yi gasar a Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai fargabar ko Brazil za ta iya samar da tsaro a lokacin gasar

Kwanaki 100 ne suka rage a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, wanda kasar Brazil za ta dauki bakuncinsa.

A wani bangare na shirye-shiryen zuwa gasar, Najeriya za ta buga wasan sa da zumunci da Mexico a Amurka, a ranar Laraba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ce ke shirya gasar duk bayan shekaru hudu.

Ana dai ci gaba da nuna fargaba game da kammala filayen wasanni da kuma ko filin saukar jiragen sama na kasar zai daukin dumbin jama'ar da za su je kallon wasan da kana ko masu zanga-zanga za su kara fitowa kan titunan Brazil a lokacin gasar.