Yobo ba zai buga wasan Nigeriya, Mexico ba

Joseph Yobo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba a taba samun yawan 'yan kallo a wasan kwararru kamar haka ba a Atlanta

Kyaftin Joseph Yobo ba zai samu halartar wasan sa da zumuncin da Najeriya za ta buga da Mexico a Atlanta, ranar Laraba ba.

Yobo mai shekaru 33 ya samu wani rauni da ba a fayyace ba, kuma an maye gurbinsa da Leon Balogun dake bugawa Jamus wasa.

Da misalin karfe (2.30 agogon Najeriya) ne za a fara taka ledar a filin wasa na Geogia Dome a Atlanta ta Amurka.

Masu shirya wasan sunce an sayar da tikitin wasan fiye da 60,000.