Hodson ya goyi bayan Cleverley

Tom Cleverley Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Wasu daga magoya baya sun fara yiwa dan wasan kiranye ta Intanet

Kocin tawagar Ingila Roy Hodgson, ya kare Tom Cleverley, bisa korafin da ake ta Intanet da cewa kar a tafi da dan wasan Manchester United gasar cin kofin duniya a Brazil.

Tun lokacin da aka rubuta korafin a Intanet, an samu sa hannun mutane sama da 12,500 dake goyon bayan kar a dauki dan wasan a cikin tawagar kasar da cewa baya kokari.

Hodgson, wanda ya saka sunan dan kwallon a karawar da za su yi da Denmark ranar Laraba ya ce "bai ga dalilin wannan kiranyen ba."

Kocin ya kara da ce wa "ya cancanci ya buga wa Ingila wasa domin yana taka rawar gani."