An dage wasan Kenya da Sudan

Kenya Team
Image caption Hukumar kwallon Kenyan ta ce ba za ta jefa 'yan wasanta cikin hatsari ba.

An dage wasan sada zumunci tsakanin Kenya da Sudan, bayan takaddama a kan filin da za su fafata da lokacin buga wasan.

Tun farko sun shirya karawa a babban birnin Sudan, Khartoum, daga baya aka dage wasan zuwa El Fasher da ke Darfur, yankin da ake samun yawan rikici.

An dawo da ranar karawa zuwa Alhamis lokacin da tawagar Kenya suka isa Sudan cikin dare.

Hukumar kwallon kafar Kenya (FKF) ta ce ba ta da masaniyar sauya filin wasan da za su kara, saboda haka ba za ta jefa 'yan wasanta cikin hatsari ba.