Ana kaurace wa wasannin Sochi

'Yan wasan zamiya na Ukraine Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin siyasan yankin Crimea ne ya shafi gasar ta Sochi

'Yan siyasa da manyan mutane da dama sun ce za su kauracewa gasar nakasassun Olympic na lokacin sanyi da za a yi a Sochi, saboda matakan da Rasha ta dauka a Crimea.

Amurka ta janye tawagarta daga gasar, wanda za a fara a ranar Juma'a.

Haka kuma kasashen Turai da dama suma sun bayyana aniyar daukar irin matakin Amurka.

Kawo yanzu dai ba san ko 'yan wasan Ukraine za su shiga gasar ba, duk da cewa sun daga tutar kasar a bikin bude gasar a ranar Alhamis.