Wilshere zai je Brazil - Wenger

Arsene Wenger da Wilshere Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wilshere zai dauki makonni 6 ne yana jinya, amma Wenger na ganin yana bukatar makonni 2 kuma ya murmure

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger ya ce "Zan yi duk abin da ya kama" domin taimaka wa Jack Wilshere zuwa gasar cin kofin duniya.

An ce Wilshere ba zai samu buga wasa ba har tsawon makonni takwas, bayan ya karye a kafarsa ta hagu a wasan Ingila da Denmark.

"Zuwa gasar cin kofin duniya na da muhimmanci ga dan wasa, saboda haka zan yi duk abin da ya kama, domin ya samu zuwa." Inji Wenger.

A ranar 13 ga watan Mayu ne a ke sa ran Hodgson zai sanar da sunayen 'yan tawagar Ingila 23 da kuma mutane bakwai masu zaman benchi.