Mun shirya karawa da Munich - Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin na hangen za su taka rawar gani a Jamus

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce doke Everton 4-1 da suka yi wasan daf da na kusa da karshe na gasar kofin FA, zai kara musu karfin gwiwar fuskantar Bayern Munich a kofin zakarun Turai.

Arsenal ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Munich a wasannin zagaye na biyu, kuma za ta ziyarci Jamus domin karawa a wasa na biyu ranar Talata.

Wenger ya ce "Nasarar da muka samu kan Everton ta kara mana karfin gwiwar shirin tunkarar Bayern Munich, musanman yadda muka taka kwallo."

Arsenal ta kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin FA ne, bayan data lashe Everton a filin wasa na Emirates ranar Asabar, rabonta da kofin tun a shekarar 2005.