Xavi na son zama kocin Barcelona

Xavi Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce a yanzu ya maida hankali wajen buga tamaula

Dan wasan Barcelona mai wasan tsakiya, Xavi, ya ce yana son ya zama kocin kungiyar bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.

Dan kwallon na Spaniya mai shekaru 34 ya kwashe tsawon wasanninsa a Barca; ya buga mata wasanni guda 700 ya lashe kofuna 22.

Xavi ya shaidawa mujallar Daily mail cewa "Ina fatan zama kocin kungiyar, amma a nan gaba, domin kwallon kafa na sani kuma ita nake son ci gaba da wakilta."

Kwantaragin dan wasan zai kare a Nou Camp a shekarar 2016, kuma yana fatan komawa cikin mahukuntan kungiyar nan gaba, amma yanzu ya maida hankali ne a taka leda kafin ya yi ritaya.

Xavi ya koma Barca daga makarantar horar da 'yan kwallo La Mesia yana da shekaru 11 a shekarar 1991, kuma ya fara wasansa karkashin kocin Holland Louis van Gaal wanda ya bashi dama a shekarar 1998.