Bincike kan kashe alkalin wasan Ghana

Ghana FA
Image caption Alkalan wasan kasar sun yi korafin rashin tsaro a filaye

'Yan sandan Ghana na binciken musabbabin mutuwar alkalin wasa Kwame Andoh-Kyei, wanda ya rasu ranar Juma'a

Iyalan mamacin mai shekaru 21, sun ce ya mutu ne sakamakon raunukan da aka yi masa, bayan karawa tsakanin kungiyar Naajoe Royals da ta Gold Stars a ranar 2 ga Maris a Bordie, a shiyyar Arewacin kasar.

Naajoe Royals ce ta lashe wasan da ci 2-0, ana zargin magoya bayan Gold Stars ne suka doki Andoh-Kyei mataimakin alkalin wasa da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Hukumar alkalan wasan Ghana ta umarci mambobinta su dakatar da aikinsu a shiyyar Arewacin kasar a wasannin kananan rukuni.

Shugaban alkalan wasa na Ghana Alex Quartey ya shaidawa sashin wasanni na BBC cewa "Ba bu matakan tsaro a yawancin wasannin Arewacin kasar, tuni muka umarci mambobinmu da su kauracewa wasanni har sai an samu tabbacin tsaro mai inganci."