Kila Kross ya koma Man United

Toni Kross Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ba ta son ta rabu da dan wasan

Dan wasan tsakiya na Bayern Munich, Toni Kross, ya bayyana sha'awarsa ta komawa buga gasar Premier idan ya amince zai bar gasar Bundesliga ta Jamus.

Kwantiragin dan wasan na Jamus ya sanya wa hannu a kungiyar zai kare a Yunin shekarar 2015, kuma ana rade radin cewa zai koma Manchester United.

Kross, mai shekaru 24, ya ce "Har yanzu ban yanke shawara kan makomata ba. Ba wani boyayyen labari ba ne ina son buga gasar Premier."

Sai dai kocin Bayern, Pep Guardiola, ya jaddada cewa baya son dan wasan ya bar Zakarun kofin Turai.