Gosling ya ce ya yi cinikin wasanni

Dan Gosling
Image caption Dan wasan ne da kansa ya ke son ya fasa kwai

Dan wasan tsakiya a klub din Newcastle Dan Gosling ya ce ya karya ka'idojin hukumar kwallon kafar Ingila da suka shafi cinikin wasanni.

Goslin, mai shekaru 24, ne da kansa ya bukaci zama da FA domin jin bayanai abin da ya aikata, hukumar FA ta ce tana tuhumar dan wasan da karya ka'idojin wasa har kala biyu.

Har yanzu ba'a tsayar da ranar fara jin bahasin ba.

Dan wasan ya koma bugawa Newcastle kwallo, bayan ya koma Blackpool aro a farkon kakar bana.

Ya buga wa Blackool wasanni a kai a kai lokacin da yake mata wasa, amma wasanni uku ya shigo sauyi tun lokacin da ya dawo Newcastle.